Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Bullar Cutar Zazzabin Lassa A Jihar Filato


Hukumar ta NCDC ta ce mutum dari da biyu ne suka mutu da cutar ta Lassa a Najeriya a bara.

Najeriya ta sami sabbin mutum 222 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa da sabbin mutum biyu a mako guda a cikin jihohi 15, ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ce ta bayyana hakan a cikin rahotonta na mako-mako a ranar Litinin.

Cutar zazzabin Lassa takan haddasa zazzabi mai tsanani dake halaka wanda ya kamu da cutar cikin kankanin lokaci, in ba’a dauki mataki da sauri ba.

Jami’ar dake kula da barkewar cututtuka masu yaduwa a jihar Filato, Matina Alex Nuwan ta ce sun tabbatar da gwajin mutum guda da ya harbu da cutar yayin da mutum tara ke jiran sakamakon gwajin cutar.

Hukumar ta NCDC ta ce mutum dari da biyu ne suka mutu da cutar ta Lassa a Najeriya a bara.

XS
SM
MD
LG