Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Cigaba A Noman Masara Bana A Jihar Kaduna


Wani Manomi a gonar shi ta masara.

Babban bankin Najeriya ya ce dalar masarar da aka kaddamar a Jihar Kaduna alama ce cewa gwamnatin tarayya ta inganta noma ta yadda za a iya fitar da masara zuwa kasashen waje.

KADUNA, NIGERIA - Dalar masarar da ta kai 21 dai manoma ne da babban bankin Najeriya ya ba su bashi su ka tara ta domin bayyana nasarar da aka samu a shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noma a kasar.

Gwamnan babban bankin Najeriya, Mr. Godwin Emefele wanda Mr. Philip Yila Yusif ya wakilta ya ce wannan dalar masara ta taimaka wajen karya farashin masara a kasuwa.

Shi kuwa shugaban kungiyar manoman masara a Najeriya Alhaji Bello Abubakar Annur Funtua cewa ya yi wannan masara ma kadan ce daga abun da aka noma bana.

Sai dai ganin kusan watanni biyar da wucewar damunar da aka noma wannan masara ya sa mai sharhi akan al'amuran yau da kullun, Comared Abubakar Aliyu Umar yin wasu tambayoyi game da wannan batun.

To amma kuma gwamna Nasuru Ahmed El-rufa'i wanda kwamishinan noma, Malam Ibrahim Husaini ya wakilta ya ce wannan shiri nasara ce ga kasa baki daya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:

An Samu Bunkasa A Noman Masara A Jihar Kaduna
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG