Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Tabbacin Amfani Da Makamai Masu Guba a Syria


Ana rububin kai mutane asibiti, wadanda suka shaki sinadarin sarin mai dauke da guba da ake zargin an yi amfani da shi a Syria
Ana rububin kai mutane asibiti, wadanda suka shaki sinadarin sarin mai dauke da guba da ake zargin an yi amfani da shi a Syria

Wata Hukumar da ke sa ido kan makamai masu guba a duniya ta tabbatar da cewa an yi amfani da sinadarin Sarin mai guba a wani mummunan harin da aka kai kwanan nan a kasar Syria.

Wata sanarwa da hukumar dake sa ido kan amfani da makamai masu guba ta kasa da kasa ta fitar (OPCW) a yau Juma'a, ta tabbatar da cewa a binciken da ta gudanar, ta gano an yi amfani da makamin Sarin mai guba a farmakin da aka kai ranar 4 ga watan Afirilu a garin Khan Shaykhun dake Syria.

Da yake Magana kan lamarin, shugaban cibiyar, Ahmet Uzumcu, ya ce “Da kakkausar murya na yi Allah wadai da wannan harin rashin imanin, wanda ya sabawa tsarin yarjejeniyar makamai masu guba.

Ya kara da cewa "kuma dole ne duk masu hannu a wannan mummuman aiki a tabatta a hukuntar da su kan abinda suka aikata.”

Ana sa ran cewa binciken hadin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da hukumar ta OPCW zai yi kokarin gano ko su waye suke da hannu a harin, wanda ya yi sanadiyar asaran rayukan mutane 87, ciki har da kananan yara da mata.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka a wata sanarwa da ta fitar ta nuna cikakken goyon bayanta ga binciken da ake gudanarwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG