Accessibility links

An Samu Wadanda Suka Kamu Da Polio 9 A Najeriya Cikin Mako Guda


Ana diga maganin rigakafin kamuwa da cutar Polio ma wani yaro dan shekara hudu da haihuwa a Najeriya

A bayan da aka shafe makonni biyu babu rahoton sabbin kamuwa da cutar Polio, sai gas hi a makon farko na watan Yuli an samu yara 9 da cutar a Najeriya

A Najeriya, yara tara ne suka nuna alamun kamuwa da kwayar cutar Polio, bayan da aka shafe makonni biyu babu labarin wata sabuwar bullar cutar ko guda daya.

Alkaluman da Shirin yaki da Cutar Polio ta Duniya (Global Polio Eradication Initiative) ya bayar sun nuna cewa an samu bullar cutar duk da kyamfe da aka gudanar na bayar da rigakafinta daga ranakun 6 zuwa 9 ga watan nan na Yuli a jihohin arewa da kuma tsakiyar Najeriya.

A yanzu haka dai, wannan yana nufin cewa Najeriya it ace ta biyu wajen yawan wadanda suka kamu da cutar Polio a bana, a bayan kasar Somaliya. Sauran kasashen da aka samu rahotannin bullar cutar ta Polio a bana sune Kenya makwabciyar Somaliya, da Afghanistan da kuma Pakistan.

Shirin yaki da cutar Polio yace ana samun ci gaba a kokarin bayar da maganin rigakafin Polio, OPV, kuma a zagaye uku na baya da aka gudanar, an samu nasarar kaiwa ga kasha 79 cikin 100 na yaran da aka yi niyya a fiye da rabin yankunan da aka gudanar da wadannan ayyuka.

Alkaluman sun nuna cewa zagaye na baya-bayan nan da aka gudanar ya fi burgewa, domin an bayar da maganin ga yara miliyan daya da dubu dari biyar da casa’in, daga ciii
Kin yara miliyan daya da dubu dari shida da aka yi niyya.
XS
SM
MD
LG