Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Ana Amfani da Makamai Wajen Kwace PVC


Na'urar Karanta PVC

Yanzu haka dai baya ga batun siyan katunan zabe da ake zargin wasu nayi, wani batu daya bullo shine na shiga gidajen mutane ana kwace masu katunan zabe, kamar yadda yake faruwa a jihar Adamawa.

Reverend, Pinas Padiyo. Kakakin jam’iyyar, APC, a jihar Adamawa, yace “da dare wasu mutane su hudu dauke da makamai, sai suka tada duk mutanen gidan da suka shiga, suka ce tunda an san su ‘yan APC, ne ba za’a barsu suyi zabe ba saboda haka kowa ya kawo katin zabe, ko a hallaka shi.”

Mr. Padiyo ya kara da cewa “Mun rubuta wa Kwamishinan ‘yan Sanda, da Daraktan ‘Yan Sandan Ciki wato SSS da mataimakin sufeton ‘yan Sanda mai kulla da wannan yanki da shi kansa Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, da kuma hukumar zabe.”

Rudunar ‘yan sandar jihar na cigaba da binciken lamarin, ta kuma shawarci jama’a, dasu kai rahoton duk wani mai saye ko kwace katunan zaben a hannun mutane.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG