Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sassauta Dokar Hana Fita A Jos


Gwamnan jihar Filato Samuel Lalong (Facebook/Gwamnatin Filato)

Saka dokar ta biyo bayan rikici da birnin Jos ya fuskanta a ‘yan kwanakin nan wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da asarar dukiyoyi.

Gwamnatin jihar Filato a Najeriya ta sake sassauta dokar hana fita a Jos ta Arewa tare dage dokar hana zirga-zirgar keke-Napep a yankin.

Wata sanarwa da Darektan yada labaran gwamnatin jihar ta Filato, Dr. Makut Simon Macham ya fitar, ta ce daga yanzu, dokar hana fitar za ta fara aiki daga 10 na dare zuwa 6 na safe.

“Gwamna Simon Lalong, ya amince dokar ta fara aiki ranar Laraba 8 ga watan Satumba 2021.” Sanarwar ta ce.

Hukumomin jihar sun ce an dauki wannan mataki ne bayan wani taro da majalisar tsaron jihar ta yi a ranar 7 ga watan Satumba, inda aka duba yanayin tsaro a birnin na Jos.

Mashinan Keke-Napep (Facebook/PLSG)
Mashinan Keke-Napep (Facebook/PLSG)

A karshen watan Agusta aka saka dokar hana fita har tsawon sa’a 24, daga baya aka sassauta ta koma 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Saka dokar ta biyo bayan rikici da birnin Jos ya fuskanta a ‘yan kwanakin nan wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da asarar dukiyoyi.

“Kazalika, daga ranar Laraba 8 ga watan satumba 2021, an dage dokar hana zirga-zirgar keke-napep inda yanzu za su rika aiki daga 6 na safe zuwa 6 na yamma.” Sanarwar ta kara da cewa.

Gwamna Lalong ya kuma yi kira ga al’umar jihar da su ci gaba da ba gwamnatin hadin kai wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya a jihar.

XS
SM
MD
LG