Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Soke Zaben Fidda Gwani Na Jam'iyyar APC A Jihar Legas


Bayan da masu zabe suka shafe lokuta da dama suna zaben fidda gwani na gwamna a tutar APC a jihar Lagos, 'yan kwamitin lura da zaben sunki amincewa da zaben tare da soke shi,kuma basu fadi ranar sake wani zaben ba, abinda magoya bayan wani dan takara ke zargin akwai lauje cikin nadi.

Shugaban kwamitin fidda gwanin takarar gwamna a jihar legas Mr. Clement Ebere ya bayyana soke zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a jihar Legas inda yace kwamitin a shirye take da ta gudanar da zabe mai tsafta wanda zai samu amincewar kowane bangare daga cikun 'yan takarar na jamiyyar APC.

Ya sjhaidawa yan jaridu cewa sun soke zaben ne domin kuwa har zuwa yammacin Talata basu samu cikakkun sunayen wakilan daya daga cikin 'yan takarar da doka ta bada umarnin ace suna da shi ba, sai dai bai bayyana wanne daga cikin 'yan takarar bane.

Zaben dai anayi tsakanin Babajide Olu ne dake samun goyon bayan shugaban jamiyyar ta APC Asiwaju Bola Tinubu da kuma gwamnan jihar Akinwome Ambode.

Saurari rahoton Babangida Jibril domin karin bayani..

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG