Accessibility links

An Tsara Sabuwar Dabarar Yaki Da Polio A Duniya

  • Garba Suleiman

Tarukkan inganta kiyon lafiya na gidan rediyon murkyar Amurka (VOA) a biranen kaduna da minna na Nigeria

Ministocin lafiya na kasashen dake Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya, ciki har da Najeriya, sun amince da sabuwar dabarar yaki da Polio.

Ministocin kiwon lafiya da wakilai daga kasashe 194 dake cikin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, cikinsu har da Najeriya, sun amince da sabuwar Dabarar Kawar da Cutar Shan Inna ta Polio ta 2013 zuwa 2018.

Jami'an sun yi rokon da a bayar da cikakken kudin aiwatar da wannan shirin domin tabbatar da cewa an ga bayan wannan cuta.

Ministocin, wadanda suka halarci Taron Kiwon lafiya na Duniya na 66 a Geneva dake kasar Switzerland, sun nuna gamsuwa da ci gaban da aka samu a shekarar da ta shige wajen rage wannan cuta zuwa matsayin da bai taba saukowa ba, a saboda irin matakan da kasashe ke dauka.

A makon da ya gabata ga misali, ba a samu rahoto ko kwaya daya na kamuwa da cutar Polio a duk fadin Najeriya ba.

Kasidar baya-bayan nan ta mako-mako da ake bugawa kan yaki da cutar Polio, Weekly Polio Update, ta ce a cikin makon da ya gabata, ba a samu sabon rahoto na kamuwa da kwayar cutar polio jinsin WPV ba.

Ta ce yawan wadanda suka kamu da wannan kwayar cutar a 2013 yana kan 22 ya zuwa wannan lokacin. Mutane na baya-bayan nan da aka samu da kwayar cutar Polio ta WPV sun bulla ne a jihohin Borno da Taraba a karshen watan Afrilu.
XS
SM
MD
LG