Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Umarci Kimanin Mutane Miliyan 40 Su Zauna A Gidajensu A California


California coronavirus

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar annobar cutar coronavirus da ta bazu ko’ina a fadin duniya ya zarta dubu 10, a yayin da cutar ta kama mutane da dama.

A jiya Alhamis gwamnan jihar California dake Amurka, Gavin Newsom, ya ba mazaunan jihar su kimanin miliyan 40 umarnin su zauna a gidajensu, a zaman wani bangare na yaki da yaduwar cutar coronavirus.

Newsom ya ba da umarnin ne biyo bayan mutuwar mutane 19, da kuma wasu da bincike ya tabbatar sun kamu da cutar a California.

Dakatar da zirga-zirga a fadin jihar na zuwa ne bayan da gundumar Los Angeles ta ba da umarnin rufe dukkan shagunan sayar da kayayyaki da wasu manyan kasuwanni da filayen wasa.

Newsome ya kuma bukaci majalisar dokokin Amurka ta amince da fitar da kudi dala biliyan daya daga kason asusun gwamnatin tarayya, domin biyan kudin jinya ga wadanda cutar ta kama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG