Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Watsama Jama'a Barkonon Tsohuwa, Da Ruwan Zafi A Kan Titi


Dubban mutane ne su ka fito kan titi suna zanga-zanga, na kin amincewa da karin kudin haraji a birnin Faris dake Kasar Faransa.

Yau Asabar Dubun-dubatar mutane ne ke zanga-zanga a sanannen titin birnin Faris, jami’an ‘yan sanda na harba musu barkonon tsohuwa da ruwan zafi, bayan sun tsallake shingen tsaro.

Wannan shine karo na uku a cikin makonni uku da jama’ar ke yin zanga-zangar, biyo bayan karin kudaden haraji da akayi, musamman akan man-fetur, da kuma gazawar shugaban kasar Emmanuel Macron.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press, ya ruwaito cewar duk tashoshin jiragen kasa dake kusa da wajen taron na Champs Elysees, an rufesu saboda tsaro.

Mafi akasarin masu zanga-zangar suna sanye da riga mai ruwan kwai, dake da alamun wuta, wadda ake amfani da ita a motocin haya.

A satin da ya wuce ne masu zanga-zangar su kayi Aron-gama da jami’an ‘yan sanda, hukumomin sunce sama da mutane 8,000 ne su ka fito a birnin da ake kira Light City, a satin da ya gabata, wasu kuma sama da 100,000 a sauran sassan kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG