Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Mexico Na Shirin Hukunta Masu Tada Rigima A Kan Iyakarsu


Iyakar Amurka da Mexico
Iyakar Amurka da Mexico

Hukumomin Amurka da Mexico sun yi alkawarin hukunta duk wadanda aka samu da laifin tayar da fitina a bakin iyaka, bayan wata zanga-zangar lumana kan tsawon lokacin da ake dauka wajen basu izinin mafaka.

Zanga zangar ta yi sanadiyar wasu gungun bakin haure suka bankade shingayen da aka saka, lamarin da yasa jami’an kan iyaka na Amurka suka harba barkonon tsohuwa.

Sakatariyar harkokin tsaron cikin gida, Kirstjen Nielsen, ta ce wasu daga cikin gungun bakin haure ne suka afkawa jami’an Kwastam da na kan iyaka, wanda hakan yasa jami’an yin amfani da barkonon tsohuwa domin kare kansu da lafiyarsu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya goyi bayan dalilin da jami’an suka bayar, yana mai cewa “Mutane ne masu karfi suka afka musu, su kuma su ka yi amfnai da barkonon tsohuwa.” Ya kuma sake maimaita kudurin gwamnatinsa, yana cewa babu wanda zai shigo mana ‘kasa sai dai ta hanyar bin ka’ida.

Ministan harkokin cikin gida na Mexico ya fada a wata sanarwa cewa hukumomi sun cafke wani gungun bakin haure da yawansu ya kai 500, wadanda suka yi kokarin kutsawa Amurka ta karfi, kuma duk wadanda aka samu da laifin hakan za a mayar da su kasashen su na asali cikin gaggawa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG