Accessibility links

An Yankewa Wani Mutum Hukumcin Daurin Shekaru 45 Domin Satar Wayar Gwamna

  • Grace Alheri Abdu

'Yan Sandan Najeriya sun mamuke wani mutum
Kotun dake zama a Osogbo jihar Osun ta yankewa wani mutum mai suna Kelvin Igbodalo hukumcin daurin shekaru 45 a gidan yari sabili da satar wayar salula ta gwamnan Rauf Aregbesola da aka kiyasta kudinta a kan Naira 50,000 a lokacin rantsar da shi.

An tuhumi Kelvin da aikata laifuka shida da suka hada da yin sojan gona, da sata, da zamba cikin aminci da kuma damfara.

Mutumin da ake tuhuma da satar wayar ya yi amfani da ita wajen damfarar Oba Gabriel
Adekunle Aromolara, Owa Obokun na Ijesha naira 500,000, yayinda ya kuma damfani wani Naira 200,000.

Wakilinmu Hassan Umaru Tambuwal ya nemi ra’ayoyin wadansu mazauna jihar Osun dangane da wannan hukumcin.

XS
SM
MD
LG