Accessibility links

Kwamitin Da Gwamnonin Arewacin Najeriya Suka Kafa Ya Mika Rahoto

  • Grace Alheri Abdu

Wani jami'in tsaro kenan a wani wurin da 'yan Boko Haram su ka kai hari
Kwamitin da gwamnonin arewacin Najeriya suka kafa domin bincike masababin tashe tashen hankali da ake fuskanta a yankin ya mika rahotonsa.

Kwamitin da Jakade Zakari Ibrahim ya jagoranta ya mika rahoton ne bayan ya shafe watanni takwas yana aiki.

Daga cikin matsalolin da kwamitin ya tarar akwai, talauci, da rashin aikin yi musamman tsakanin matasa.

A cikin hirarsu da wakiliyarmu Madina Dauda shugaban kwamitin ya bayyana kwarin guiwa cewa gwamnonin zasu maida hankali wajen aiwatar da shawarwarin kwamitin, yayinda a nasu bangaren gwamnonin suka yi kira ga al’umma su bada hadin kai domin nasarar shirin.
XS
SM
MD
LG