Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Gagarumar Nasarar Samun Rigakafin Coronavirus - Trump


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yabawa ci gaban da ake samu wurin samar da maganin rigakafin coronavirus a jiya Juma’a, a jawabinsa na farko a bainin jama’a tun bayan lokacin da kafafen yada labarai suka ce tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya lashe zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.

Trump da yaki amincewa da shan kaye a zabe, ya yi jawabin nasa ne daga fadar White House amma kuma bai amsa tambayoyi daga manema labarai ba.

Ya kira aikin samar da maganin da mafi girma da aka taba gani a tarihin samar da rigakafi a Amurka, yana mai cewa sau tari ana kwashe sama da shekaru takwas kafin samar da rigakafi mai inganci.

A ranar Litinin, katafaren kamfanin harhada magunguna na Pfizer, ya sanar cewa ya kirkiri maganin rigakafi mai matukar tasiri a kan coronavirus da kashi 90 cikin dari, lamarin da ya kai shugaba Trump ga fitar da sakon Twitter kamar haka “BABBAN LABARI MAI DADI.” Kamfanin da ya samar da maganin dole ne zai kammala gwaji kana ya samu amincewar Hukumar Abinci da Magunguna ta Amurka.

A cikin jawabinsa, a karon farko Trump ya bayyana tababarsa a kan rashin sanin tabbas ga gwamnati ta gaba, yana mai cewa, babu yadda za a yi gwamnatinsa ta sake kafa dokar hana zirga zirga amma kuma ya ce tana yiwuwa Biden ya kafa dokar idan ya hau mulki.

"Tana yiwuwar duk abin da zai faru nan gaba, wanda babu mahalukin da ya san gwamnati ta gaba, ina sa ran lokaci ne kawai zai tabbatar mana, amma ina tabbatar da cewa wannan gwamnati ba zata rufe kasar ba," inji Trump.

Sai dai Biden bai fada ko zai kafa dokar hana zirga zirga ba domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Amma Biden ya fada a wata sanarwa a jiya Juma’a cewa ya gana da wakilan kwamitinsa na karbar mulki masu kula da COVID-19, da suka bada bayana masu daga hankali a kan tabarbarewar kiwon lafiyar jama’a cikin gaggawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG