Accessibility links

An Yi Juyayin Mutuwar Nelson Mandela A Jamhuriyar Niger


Shugaba Nelson Mandela
A Jamhuriyar Niger jami'an gwamnati da masu zaman kansu sun yi juyayin rasuwar tsohon shugaban Afirka Ta Kudu kuma bakin mutum na farko da ya taba zama shugaban kasar.

Daga cikin mutane 'yan asalin Afirka da suka taka rawar a zo a gani to dole sai an anbato sunan Nelson Mandela ba don komi ba amma ya kasasnce mutum mai neman zaman lafiya da yin adalci da kyautatawa jama'a. Irin wadannan halaye suka sa ya zama jarumin shugaba wanda samun irinsa zai yi wuya kamar yadda wani dan siyasa a Niger Farfasa Alhaji Sanusi Tambari Jaku ya fada. Ya ce mutum ne wanda yake da hakuri. Yana da kokari kuma mutum ne wanda baya rasa imani a zuciyarsa. Ya ce mutanen da suka sashi gidan kaso har shekara 27 suka lalata masa rayuwa da gidansa ya dawo kuma ya gafarta masu ai ba'a kwatantashi da kowa.

Farfasa Ado Muhammed malamin jami'a ya ce Nelson Mandela fitila ce da ya haskaka ma Afirka hanyoyin da za'a bi a tafi da jama'a a kuma biya bukatunsu a zauna lafiya. Wannan hasken da ya bayar a kula da shi a kuma koyas da shi a cikin makarantu domin a samu a horas da 'ya'yan Afirka. Nelson ya nuna mana dabi'un kawo shiryawa tsakanin mutane da kawo zaman lafiya. Ya nuna wa mutane cewa ko mutum na kaso ya iya yiwa jama'a aiki. Idan kana kan mulki ka iya yiwa jama'a aiki . Idan ma ka sauka ka iya yiwa jama'a aiki idan dai kana da niyya ta kwarai kamar Nelson Mandela.

Abdullahi Mamman Ahmadu nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG