Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Karar Gwamnatin Trump A Kotu


Kotun kolin Amurka

Jihohi goma sha shida a nan Amurka sun kai karar gwamnatin Trump kotu game da ayyana dokar ta baci saboda ya samu kudin da zai gina Katanga a kan iyakar kasar.

Manyan lauyoyin jihohin karkasin jagorancin babban lauyan jihar California sun shigar da kara a ranar Litinin a wata kotun dake gundumar arewancin California.

Karar da su shigar na cewar ayyana dokar ta bacin ya sabawa dokoki da ma kundin tsarin mulkin kasar, haka kuma zai cutar da jihohi da mazauna cikin su idan aka dauki kudade daga fannonin yaki da miyagun kwayoyi da ayyukan gine-ginen sojoji da ma wasu ayyukan hukumomin tsaro, domin wannan aiki.

Kararrakin sun yi kira ga kotu ta hana gwamnatin Trump kwata-kwata a kan aniyar ta ta karkatar da kudaden asusu zuwa ginin bango da take niyar yi ko kuma a hana ta gina bangon ba tare da majalisun tgarayya sun bata kudi ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG