Accessibility links

An Yi Kira Ga Gwamnati Nigeria Ta Kawo Karshen Cutar Shan Inna


Sauro mai kawo zazzabi

Kungiyar mutanen da suka yi nasara da cutar shan-inna a Nigeria, sunyi kira mai karfi ga iyaye dasu kai ‘ya’yansu, kasa da shekara biyar domin a yi masu allurar rigakafi domin kiyaye su daga nakasa.

Kungiyar mutanen da suka yi nasara da cutar shan-inna a Nigeria, sunyi kira mai karfi ga iyaye dasu kai ‘ya’yansu, kasa da shekara biyar domin a yi masu allurar rigakafi domin kiyaye su daga nakasa.

Shugaban kungiyar na kasa Misbahu Lawan Didi, yace, “Duk yaron da ba a digawa maganin ba, a lokacin da ake aikin rigakafi, ya bata kokarin kariyar, kuma zai sa kansa da sauran yara cikin hatsarin kamuwa da wannan cutar.” Ya kara cewa: “cutar shan-inna ba nakasar da yaro kawai take yi ba, amma matsala ce ga dukan kasa da duniya gaba daya.”
Da yake Magana a madadin kungiyar, da ta kunshi fiye da mutane 100,000 da suka kamu da cutar a Nigeria, yace: “Nigeria ce kasar da aka fi samun cutar a Afirika. Idan muka kasa shawo kan yaduwar kwayar cutar shan-inna a nan, to dukan sauran kasashe suna cikin hadarin sake kamuwa. Ina rokon dukan shugabannin addini da al’adu su fito su tabbatar an digawa kowanne yaro ruwan maganin a kowanne zagaye.”

Kungiyar ta taimaka sosai domin karfafa cigaban yaki da cutar ta shan-inna, suna kuma kokarin shiri domin tabbatar da cewa ba a bar wani yaro a baya ba lokacin rigakafin gama gari da aka yi ranar 15 ga watan Mayu (IPD) a jahohi 15 dake arewacin Nigeria, kamin damuna ta fara.

Tun farkon wannan shekarar, yara 16 dake kasa da shekara biyar suka kamu a jahohi takwas na arewacin Nigeria, idan aka kwatanta da 40 da aka gani a jihohi 10 a shekarar 2012. Wannan ya kawo raguwar cutar, da kuma damar kawar da ita daga Nigeria kasar da tafi kowacce cutar a yankin afirika.

Masana sunce lokacin damuna shine babban lokacin da kwayar cutar ke kama kananan yara a Nigeria. Kungiyar tana kokarin yiwa mutane bayani game da rashin digawa kananan yara maganin cutar.

Hanyar nasara itace yin allurar rigakafi ga yara da damina, da kuma kare wuraren da cutar bata yadu ba a jihohi, karamar hukuma da kauyuka a lokacin rigakafin, kafin ruwan sama ya tsaya. Babbar damuwar itace sake barkewar cutar, da matsalar tsaro musamman a jahohin Borno da kano wadanda suka hana ma’aikata shiga wurare da ke da kasadar kamuwa.

Masana sunyi gargadi da cewa, idan ba a sami nasarar kauda cutar shan-inna a yunkurin ta kasa ya kasa da ake yi ba, kananan yara 250,000 zasu kamu da cutar ko kuma su mutu ta dalilin kamuwa da cutar.
XS
SM
MD
LG