Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Kira Ga Matasa Su Fito Su Kada Kuri'a a Zaben Zimbabwe


Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa
Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa

Wasu kungiyoyi sun maida hankali a kan matasa a Zimbabwe su shiga zaben kasar na farko, bayan saukar Robert Mugabe daga mulki da za a yi a ranar Litinin, wanda batun rashin ayyukan yi da tabarbarewar siyasa zasu zama batutuwar da masu kada kuria zasu mai da hanakali a kai.

Yayin da yan siyasa ke auna manyan birane da shahararrun wurare domin samun kuru’u kafin zaben na ranar Litinin 30 ga watan Yuli, wata kungiyar rajin ci gaban matasa ta Youth Empowerment and Transformation Trust da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, suna gudanar da nasu gangami ne a fadin kasar domin tabbatar da matsa sun shiga harkokin zabe.

A garin Mbare, wani jami’in kungiyar Trust Charles Chisale ya yi bayanin taken nan na “Ku fita Ku Kada Kuri’a”, wanda ya yi kira ga tattaunawa.

Yace zamu ci gaba da tattaunawa a kan batutuwa da suka shafi matasa, da abubuwan da suke bukata bayan zaben 2018, don haka ku fito ku saurare mu, ku fito muyi sayar ra’ayoyi ta yadda zamu gina Zimbabwe da muke muradi.

Haston Gumira wani shugaban matasa a garin da yaki ya bayyana jami’iyar da yake ciki, ya yi marhabi da wannan ra’ayi, inda ya karfafa gwiwar matasan Zimbabwe su fita su yi zabe a ranar Litinin.

Yace matasa mun sha wahala kuma yanzu wahalar ta ishe mu, yanzu lokaci ya yi da yakamatra mu yi amfanin da yawan mu, saboda kashi 60 cikin dari na adadin masu kada kuri’a miliyon biyar da dubu dari biyar matasa ne yan shekaru daga 18 zuwa 40, don haka yakamata mu yi amfani da wannan dama saboda a matsayina na matashi na san matsalar matasa iri daya ne, shi yasa idan zamu yi zabe to mu maida hankali a batun da suka shafe mu da batun rashin aikin yi.

A zaben na ranar Litinin, shugaban kasar Emmerson Mnangagwa mai sheakru 75, zai kara ne yan takara 22, ciki har da Nelson Chamisa mai shekaru 40 dake jagorantar jam’iyar Democratic Change Alliance.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG