Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kai Farmaki Kan Mayakan ISIS Dake Garin Mosul


Wasu dake kokarin ficewa daga garin Mosul
Wasu dake kokarin ficewa daga garin Mosul

Dakarun Iraqi na Musamman sun kama tashar talabijin din kasar dake Mosul, a wani kokari na sake kwato garin daga hannun 'yan kungiyar ISIS.

Wani Janar din mayakan Iraqi ya ce dakarun kasar na musamman sun kama tashar talabijin din kasar dake Mosul, a zaman wani bangare na farmaki da suka auna kan birnin da zummar korar 'yan kungiyar ISIS.
A karon farko tun shekarar 2014, sojojin Iraqi suka shiga birnin, bayan da suka fi maida hankali kan kauyuka da suke ciki da kewayen birnin na Mosul.
Manjo Janar Sami al-Aridi ya fadi cewa dakarun sun shiga unguwar Gojali dake Mosul a safiyar yau Talata, inda suka yi bata kashi da mayakan ISIS.
Ya kuma ce mayakan na ISIS sun gina shingaye na kankare don hana dakarun Iraki shiga birnin.
Zafafan hare-hare ta sama kan inda mayakan na ISIS suke a unguwannin Gojali sune suka bude hanya ga dannawar da dakarun Iraki suka yi. Mayakan sun maida murtani ta harba makamai masu linzami da kuma gurneti.
Wannan nasarar na zuwa ne makonni 2 bayan da hadakar dakarun kurdawa, da na ‘yan shi’a, da kuma barin wuta ta sama da dakarun Amurka suka kaddamar a matsayin farmaki mafi girma a kasar tun bayan shekarar 2003, don kawas da ‘yan ISIS.

XS
SM
MD
LG