Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola: Maganin Rigafin Cutar Zai Taimaka Sosai Wannan Karon


Rayuka da dama sun salwanta a shekarun baya sakamakon bullar cutar Ebola, amma maganin rikafin cutar da aka samo yanzu zai taimaka matuka wajen dakile cutar.

Cutar Ebola da ta kashe sama da mutane 20 a arewa maso gabashin Janhuriyar Dimokaradiyya Congo, tana iya yin barna kamar wadda aka yi fama da ita shekarun baya a Afrika ta Yamma, idan ba a dauki mataki ba.

Sai dai masu agajin farko sun ce a wannan karon, lamarin ya sake, sabili da sun sami maganin rigakafi yanzu, da ba a iya amfani da shi ba a shekara ta 2013, lokacin da aka sami bullar cutar Ebola ta farko a kasar Guinea.

Kamfanin sarrafa magunguna na Merck ya tura maganin rigakadi da ake kira V920 guda dubu takwas da dari shida zuwa yankin da cutar ta bulla. An yi gwajin maganin rigakafin a matakai uku sai dai ya zuwa yanzu, babu kasar da ta bada lasisin amfani da shi .

Kakakin hukumar lafiya ta Duniya ya shaidawa Muryar Amurka cewa, hukumar zata yi amfani da maganin rigakafin a Janhuriyar dimokradiyyar Congo.

Kawo yanzu, maganin rigakafin V920 ya hana kowa kamuwa da kwayar cutar Ebola. A lokacin da aka yi gwajin maganin a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, babu ko mutum guda daga cikin mutane dubu biyar da dari takwas da talatin da bakwai da aka yiwa rigakafin da ya yi rashin lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG