Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Tallafawa Arewa Maso Gabas


'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.

Kungiyoyin addinai da cibiyoyin ilimi a Najeriya sun fara daukan matakan farfado da harkar ilimi a arewa maso gabashin kasar, yayin da mazauna yankunan da aka kwato daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram ke shirye-shiryen komawa gidajensu

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Modibbo Adama da ke Yola a kirkiro sabon shirin bada gurbin karatu. Farfesa Kyari Muhammed, shine shugaban jami’ar kuma ya bayyana dalilan daukar wannan mataki.

“Akwai wuraren da shekaru uku, hudu ba su yi noma ba, dama sai an yi noma sannan ake baiwa yara kudi su yi karatu”.

Ita ma a nata gudun muwar, kungiyar Izala ta fitar da nata shirin, kamar yadda shugaban kungiyar a Najeriya Abdullahi Bala Lau ke cewa:

“Muna da gudun muwar da zamu bada wurin tabbatar da farfado da ilimin da ya tabarbare saboda rashin zaman lafiya. Saboda haka duk abun da zamu iya yi, don mu tallafa wa gwamnati a ga cewa ilimi ya inganta, ilimi ya dawo zamu yi. Ba kawai taimakon gwamnati bane, taimakon kan mu ne.”

Kamar yadda alkaluman hukumomin bunkasa harkar ilimi ke nunawa, daruruwan makarantu ne ‘yan Boko Haram suka lalata, baya ga daliban da aka kashe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG