Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba da Yaba Zaben Osinbanjo Mataimakin Buhari


Dan takarar Shugaban Nijeriya karkashin Jam'iyyar APC Janar Muhammadu Buhari.
Dan takarar Shugaban Nijeriya karkashin Jam'iyyar APC Janar Muhammadu Buhari.

Ana cigaba da yaba zaben Furfesa Yemi Osinbanjo Mataimakin Dan Takartar Shugabancin Nijeriya karkashin jam'iyyar APC.

Ganin yadda wanda aka zaba Mataimakin Dan Takarar Shugaban Nijeriya karkashin Jam’iyyar APC Furfesa Yemi Osinbanjo ya fito ne daga yankin Yarbawa mai yawan kuri’u, wanda kuma fitaccen Kirista ne, hakan ya sa jam’iyyar ta kauce ma matsalar tsayawa takarar mabiya addini guda, wanda hakan ya sa wasu ‘yan jam’iyyar ta APC murna sosai, inji wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhekaya.

To saidai dan takarar Shugaban Nijeriya karkashin APC, Janar Muhammadu Buhari (murabus) ya fi fifita cancanta bisa addini. Don haka, da aka tambaye shi ko ya gamsu ganin mataimakinsa Kirista ne a maimakon Musulmi, sai Buhari, wanda ko a zaben 2011 ya tsaya ne da Rev. Tunde Bakare, ya ce masu saka batun addini isgilanci kawai su ke yi.

Wani mai suna injiniya Abdullahi Aliyu daga jihar Borno y ace Jam’iyyar ta yi abin da ya dace saboda zabar Furfesa Yemi Osibanjo. Ya ce da alamar za su hada kai da Tunde Bakare. Shi kuwa Bashir Bukar Bala Sakataren Kampe din Janar Muhammadu Buhari a jihar Yobe, ya ce su yarbawa da Musulminsu da Kiristansu, da ma wadanda basu da addini, a dunkule su ke balle ma batun Rev. Tunde Bakare da Furfesa Yemi Osinbanjo.

Ana Cigaba Da Yaba Zaben Osinbanjo Mataimakin Buhari - 2'59"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG