Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Jirar Sakamakon Zabe A Kasar Mauritania


Ma'aikatan zabe a Mauritania
Ma'aikatan zabe a Mauritania

A jiya Asabar ne al’ummar kasar Mauritania suka kada kuri’a a zaben farko da aka yi a kasar ba tare da wani shugaban kasa mai ci tun bayan juyin mulkin shekarar 2008.

An rufe runfunar zabe da karfe bakwai na yamma a fadin kasar dake yankin sahara kuma anasa ran samun sakamakon zaben ‘yan majalisar dokoki da yammacin yau.

Koda yake an samu fitowan dimbin masu kada kuri’a a wannan zabe, wanda ake gani mafi muhimmanci a tarihin demokaradiyar kasar, amma mutane da dama ne suka nuna damuwa ga hukumar zaben kasar ta CENI wacce a farkon wannan shekara taki yarda da masu sa ido daga kasashen waje, lamarin da yasa ake shakku ko zata yi aiki da gaskiya.

Ma’aikata a ofishin jakdancin Amurka suna cikin wadanda suka duba yanda aka gudanar da kuri’ar a runfunar zabe a babban birnin kasar Nouakchott.

Muna da rukunoni goma na ma’aikatan mu da suke sa ido a kan zaben tun lokacin da aka bude runfunar zabe da mislain karfe bakwai na safe a cikin babban birnin kasar, inji jakadar Amurka a Mauritania Michael Dodman, yana fadawa Muryar Amurka.

Yace zasu jira su ga yanda sakamakon zaben zai kaya kana su ji abin da masana zasu fada a kan zaben. Ya kara da cewa suna sa ran komai zai tafi daidai cikin gaggawa da kuma tabbatar da ganin mika mulki da za a yi zai kara inganta demokaradiyar Mauritania.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG