Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry Yace Yana Samun ci Gaba a shawarwarin Wanzarda Zaman Lafiya a Gabas ta Tsakiya


Sakatare Kerry da shugaban yankin Falasdinu Mahmud Abbas.
Sakatare Kerry da shugaban yankin Falasdinu Mahmud Abbas.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, yace yana samun ci gaba kan shirin wanzarda zaman lafiya a Gabas ta tsakiya, duk da haka yace har yanzu da sauran aiki.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, yace yana samun ci gaba kan shirin wanzarda zaman lafiya a Gabas ta tsakiya, duk da haka yace har yanzu da sauran aiki.

Mr. Kerry yayi magana ne jiya Asabar bayan da ya gana da shugaban yankin Falasdinu Mahmud Abbas a Ramallah dake yammacin kogin Jordan, a karo na biyu cikin kwanaki biyu. Ya bayyana fatar shugabannin Isra’ila da na yankin Falasdinawa ba tare da wani jinkiri ba zasu amince kan tsarin tafiyar da shirin neman wanzarda zaman lafiya.

Kerry yace wakilan sassan biyu sun fara “tunkarar batutuwa da suka fi sarkakiya”. Har ma aka ji wakilin yankin Falasdinu a shawarwarin Saed Erikat yana cewa ma “an kasa” ba zabi bane ga yankin Falasdinu.

Daruruwan Falasdinawa suka yi maci kan titunan birnin Ramallah ranar jumma’a suna Allah wadai d a shawarwarin wanzarda zaman lafiyar, suna cewa wata hanya ce kawai ta jan lokaci.

Haka nan a lokacin wannan ziyara Kerry ya gana da PM Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan harkokin wajen kasar Avigdor Lieberman. Ya gayawa shugabannin cewa idan suka cimma daidaito kan tsari hakan zai taimaka wajen rage sassan da ake samun rashin fahimtar juna tsakanin wakilan Isra’ila da na yankin Falsdinua a shawarwarin wanzarda zaman lafiyan.
XS
SM
MD
LG