Accessibility links

An Fara Zaben Wakilan Majalisar Dokokin a Bangladesh Cikin Tsauraran Matakan Tsaro

  • Aliyu Imam

Magoya bayan jam'iyyar Awami mai mulkin kasar suke dukar wata 'yar majalisa.

A Bangladesh an fara zaben ‘yan majalisar dokoki kasar cikin tsauraran matakan tsaro, zabenda babbar jam’iyyar hamayya a kasar BNP ta kauracewa.

A Bangladesh an fara zaben ‘yan majalisar dokoki kasar cikin tsauraran matakan tsaro, zabenda babbar jam’iyyar hamayya a kasar BNP ta kauracewa. Tarzomar tana dushe zaben nay au, ciki harda kona rumfunan zabe fiyeda 120.

Jaridar kasar da ake kira Dhaka Tribune a wani rahoto da ta buga a safiyar yau lahadi tace an lakadawa wani jami’in zabe duka har lahira a wata tashar zabe a gundumar Thakurgaon dake arewacin kasar, an raunata wasu jami’an zabe su 10 suna samun jinya a asibiti.

Babbar jam’iyyar hamayyar kasar tana kira ga jama’a kada su fito domin shiga zabenda ta kira “don kada ace ba a yi ba”, yayinda jam’iyyar Awami mai mulkin kasar zata sami gagarumar rinjaye ganin fiyeda rabin mazabu dake kasar ‘yan takara karkashin inuwar jam’iyyar basu da baokanan hamayya.

Masu sa ido na kasa da kasa sun ki tura wakilan su zuwa Bangladesh domin ayyukan sa ido.

‘Yan hamayya karkashin jagorancin tsohuwar PM kasar Khaleda zia sun bukaci PM kasar Sheikh Hasina tayi murabus, ta mika iko ga gwamnatin wucin gadi wacce zata gudanar da zaben. Taki, tana cewa bin wannan hanyar a baya babu abunda ya haifar illa rashin zaman lafiya.
XS
SM
MD
LG