Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Gudanar Da Zaben Majalisar Dokoki A Ukraine


Shugaban Ukraine- Volodymyr Zelenskiy

Sabuwar jami’iyar da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya kafa ta nada Dmytro Razumkov a matsayin mai bada sahawara a kan harkokin yakin neman zabe, yayin da take shirin yiwa masu neman yiwa jami’iyar takarar majalisar dokoki a cikin watan Yuli tambayoyi, inji wakilan jami’iyar.

Razumkov, darektan wani kamfanin bada shawarwari a kan harkokin siyasa, ya fara shiga siyasa ne a matsayin tsohon dan jami’iyar tsohon shugaban kasar mai kawance da Rasha Viktor Yanukocych, wanda zanga zangar Maidan ta kawo karshen mulkin sa ya kuma arce zuwa Rasha a shekarar 2014.

Dan wasan barkwancin da bashi da wata kwarewar siyasa a baya, Zelenskiy ya ba shugaban kasar kashi da rata mai yawa a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a ranar 21 ga watan Afrilu.

Wuni guda bayan an rantsar da shi a ranar 20 ga watan Mayu, ya sanya hannu a kan dokar da ta rusa majalisar dokoki kana ya ajiye ranar 21 ga wata Yuli a gudanar da zaben majalisar.

Yin zabe da wuri zai baiwa Zelenskiy dama samun tasiri a farko farko wa’adinsa na shekaru biyar, ta hanyar samun goyon baya a majalisar kasar mai yawan al’umma miliyan 44, wacce take kara fuskantar matsin lamba daga Rasha, kana tana fama da matsalolin tattalin arziki da cin hanci da rashawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG