Accessibility links

Ana Yada Bayanai Marasa Tushe Kan Abubuwan Da Suka Faru A Baga


Shugaban tawagar bincike ta rundunar sojojin Najeriya kan Baga, Manjo-janar Lawrence Ngubani, yana magana lokacin wani taro a Maiduguri.

Kakakin rundunar tsaron hadin guiwa, Kanar Sagir Musa, ya kalubalanci duk wanda ke cewa daruruwan mutane suka mutu da ya nuna shaidarsa.

Kakakin rundunar tsaron hadin guiwa ta kasa da kasa dake bakin iyakar Najeriya da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar, ya bayyana cewa babu abinda masu son tayar da fitina ke juyawa domin cimma muradunsu, kamar irin fitinar da ta faru a garin Baga, inda ake ta yada labarai marasa tushe ko hujja kan adadin mutanen da suka mutu.

Kanar Sagir Musa, yace adadin mutanen da suka mutu a fitinar ta Baga, ya saba sosai da ainihin abinda ya wakana, yana mai bayyana cewa idan akwai wanda ya san inda kaburburan daruruwan mutanen da aka kashe suke, to ya zo ya nuna musu ko ya nuna ma duniya.

Kanar Sagir Musa, ya kuma yi bayani dalla-dalla na abubuwan da suka faru, da kuma lokutan da suka faru din:

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG