Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare Hakki Ta Ce Hotunan Tauraron Dan Adam Sun Nuna Mummunar Barna A Baga


Wani bangare na gidajen da suka kone a garin Baga, wanda aka dauka da tauraron dan Adam ran 26 Afrilu, 2013.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce hotunan sun nuna gidaje 2,275 wadanda suka lalace a unguwannin fararen hula na garin Baga.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Human Rights Watch" ta ce hotunan da aka dauka da tauraron dan Adam sun nuna "barna mai yawan gaske" a yankunan fararen hula a wani gari na arewacin Najeriya inda dakarun tsaron gwamnati da masu kishin Islama suka gwabza fada a watan da ya shige.

Kungiyar ta fada yau laraba cewa hotunan sun nuna gine-gine dubu 2 da 275 da aka lalata a garin Baga, dake Jihar Borno. ta ce mutanen garin sun dora laifin lalata wadannan gidaje a kan sojojui wadanda aka yi zargin sun kai farmakin daukar fansa kan garin a bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari kan sojoji masu sintiri suka kashe soja guda daya.

Rundunar sojojin Najeriya ta fada a makon jiya cewa gidaje kimanin talatin kawai suka kone, suka kuma ce 'yan Boko Haram ne suka kona su. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an kashe mutane 187 a wannan fada, adadin da shi ma rundunar sojojin ta Najeriya ta karyata.

Kungiyar Human Rights Watch ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin. Darektanta mai kula da al'amuran nahiyar Afirka, Daniel Bekele, ya ce "mummunan sabanin da ake gani" a tsakanin rahotannin dake fitowa daga garin Baga, da kuma wadanda ake ji daga bakin jami'an sojan Najeriya, yana haddasa damuwar cewa sojojin su na kokarin boye cin zarafin jama'a da suke yi ne.
XS
SM
MD
LG