Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Antonio Guterres Ya Bukaci Amurka Kada Ta Fice Daga Yarjejeniyar Paris


Antonio Guterres.
Antonio Guterres.

A jiya Talata ne babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci gwamnatin Donald Trump da kada ta fice daga yarjejeniyar sauyin yanayin da aka cimma ta Paris, yana mai cewa yarjejeniyar na da muhimmanci ga tattalin arzikin Amurka da tsaronta.

Da yake magana gaban wasu ‘daliban jami’ar New York, Gueterres ya nemi wannan bukata ne ga gwamnatin Amurka, wanda ya ce nan gaba za'a san shawarar da Amurkar ta yanke, ko ta fice ko kuma ta ci gaba da kasancewa cikin yajejeniyar da aka kula tun shekarar 2015.

Guterres, kwararren ‘dan siyasa kuma ma’aikacin diplomasiyya, yace yana magana da gwamnatin Amurka da ‘Yan Majalisu domin ya shawo kansu wajen nuna musu wannan abu ne mai muhimmanci ga Amurka idan ta kasance cikin yarjejeniyar, wadda ake ganin zata rage dumamar yanayi zuwa yadda yakamata ta kasance.

A lokacin da Guterres ke jawabin, yace “shaidar da zan bayar a yau itace matukar muhimmancinta ne yasa kasashen duniya suka samar da yarjejeniyar sauyin yanayi, ta Paris, kuma muna kokarin ganin mun sami nasara.”

Ya ce babu juyayin kan ilimin kimiyya, yanzu haka ana ganin illar dumamar yanayi a duk fadin duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG