Accessibility links

Anyi musayar harbe-harben bindigogi a Bulunkutun Maiduguri

  • Haruna Biu

Jami'an tsaro ke gadi domin hana tashin hankali a birnin Maiduguri jihar Bornon Nigeria.

Wasu Mazauna unguwar Bulunktu dake Maiduguri, jihar Bornon Nigeria sun kwana cikin Zullumi da fargaba sakamakon karar bindigogi da musayar harbe harbe-harbe tsakain jami’an tsaron hadin gwiwa da wadanda ake kyautata cewar mayakan ‘yan Boko haram ne.

Saurari:

A duk lokacin da aka sami irin wannan musayar harabe-harbe, mazauna unguwa kan fice ne daga unguwa zuwa wata unguwar ta dabam saboda tsoron abinda ka kai ya komo.
Ko a musayar wutar ran litinin, saida wasu mazauna unguwar Bulunkutun suka tattara nasu ya nasu suke fice daga unguwar sakamakon zargin da suka yin a cewar jami’an tsaro sun harbi mutane biyu a akafa, kuma daga daga cikin mutaten biyu ya rasa ransa sakamakon harbin kamar yadda jagoran mazauna unguwar kuma shaidar gani da ido Alhaji Bashir ya shaidawa wakilin muryar Amurka (VOA).

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG