Accessibility links

Anyi Musayar Wuta Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Bindiga A Poteskum

  • Aliyu Imam

Gwarwakin mutane da ake zargin 'Yan Boko Haram ne suka halaka su.

Sakamakon musayar wuta da bindigogi tsakanin ‘Yansanda da mutane da ba a san ko su wanene ba a Poteskumo cikin jihar Yobe cikin daren jiya Jumma a, shaidu suka ce....

Sakamakon musayar wuta da bindigogi tsakanin ‘Yansanda da mutane da ba a san ko su wanene ba a Poteskumo cikin jihar Yobe cikin daren jiya Jumma a, shaidu suka ce mazauna yankin sun gudu daga gidajensu domin neman mafaka.

An bada rahotanin jin harbin bindgigoi kusa da caji ofis na Yan Sanda da wasu sassan garin, har da labarin fadan ya rutsa da wadansu ko da yake ba a tabbatar da labarin wadanda fadan ya rutsa dasu ba.

Potsekumo yana daga cikin yankuna 15 d a shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci cikin makon jiya, kwanaki bayan an kai wasu munanan hare hare cikin kasar.

Fadan da ya barke da asubahin yau ya biyo bayan hare hare da ‘yan bindiga suka kai har suka kashe akalla mutane ashirin a arewa maso gabshin kasar.

Harin da aka kai jiya jumma ya auku ne Mubi cikin jihar Adamawa, kusa da kan iyakar kasar da kamaru. Wani dan jarida a yankin ya gayawa sashen hausa cewa ‘yan bindigan sun bude wuta a sassa daban daban uku. Rahotanni daga yankin an auna hare haren ne kan ‘yan kabilar Igbo.

Wani mutum da ake kira Habu Qaqa dake ikirarin shine kakakin kungiyar Boko Haram yace kungiyar ce take da alhakin harin da aka kai kan wani coci a Gombe daren Alhamis har aka kashe mutane shida da jikkata wasu 10.

Kakakin Boko Haram din yace harinya biyo bayan wa’adi da kungiyar ta bayar cikin makon nan inda ta bukaci dukkan kiristoci su fice daga arewacin Najeriya da galibinsa musulmi ne.

Sakamakon harin da aka kai cikin karamar hukumar Mubi,gwamnatin jihar Adamawa ta kafa dokar hana yawo,kamar yadda zaku ji cikin wan nan rahoto da wakilinmu Ibrahim Abdul aziz ya aiko mana.

Ahalin da ake ciki kuma, wani alkali anan Amurka ya jinkirta yanke hukunci akan dan Najeriyan nan Umar Farouk Abdulmutallab wanda yayi yunkurin tarwatsa jirgin fasinjar Amurka da bai sami nasara ba.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG