Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Ya Gabatar Da Shirin Tsuke Bakin Aljihun Gwamnati


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya na yiwa 'yan kasa jawabin sanar mu su da cewa tare da jami'an gwamnatin kasar za a sha wahalar tsadar rayuwa

Ya ce za a takaita tafiye-tafiyen jami’an gwamnati kuma za a rage mu su albashi da kashi 25 cikin dari

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana ta talbijin a jiya Asabar inda ya yi alkawarin cewa tare da gwamnatin kasar za a sha wahalar matsalar tsadar man da talakawan kasar ke fama da ita.

Mr.Jonathan ya ce lallai ne kowa ya yi damarar sadaukar da wani jin dadin rayuwa. Ya ce za a yi matukar takaita tafiye-tafiyen jami’an gwamnati kuma za a rage mu su albashi da kashi 25 cikin dari.

Shugaban yayi jawabin ne ta talbijin din gwamnatin kasar Najeriya, a gabannin yajin aikin gama garin da aka shirya yi a kasar saboda hauhawar farashin man fetur. Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun yi sanarwar shiga yajin aikin sai baba ta gani daga gobe Litinin.

Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi bayan da gwamnatin kasar Najeriyar ta cire tallafin man tun ranar daya ga watan nan na janairu, wanda hakan ya janyo tsadar sufuri da tsadar kayayyakin abinci.

Mako daya kenan da ‘yan kasar Najeriya da ke harzuke su ka fara yin zanga-zanga, kuma a Abuja babban birnin tarayyar kasar an samu zanga-zangar da ta yi muni.

Amma wasu masana ilimin tattalin arziki sun ce tallafin mai ya na karfafa rashawa da cin hanci.

Najeriya babbar mai arzikin danyen man fetur ta dogara kusan baki daya akan sayen mai daga waje saboda matatun man kasar sun lalace sanadiyar rashin iya aiki da kuma ha’inci.

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG