Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Azumi: Shugabannin Jama'a Na Cigaba da Kiran A Zauna Lafiya


Sallah lokacin azumi
Sallah lokacin azumi

A yayinda ake cigaba da azumin watan Ramadan shugabannin jama'a na cigaba da kira ga 'yan Najeriya da su zauna lafiya da juna

Alhaji Hassan Magajin garin Akiyelen Ibadan cikin jihar Oyo yace babu abun da ya fi zaman lafiya dadi. Duk inda aka ce babu zaman lafiya babu wanda zai so ya je wurin saboda tashin hankali. Inda aka samu zaman lafiya za'a iya shiga a yi huldodi lafiya a kuma koma gida lafiya. Saboda haka ake rokon Allah ya kara wa kasar Najeriya zaman lafiya.

Akan alfanun zaman lafiya Alhaji Hassan yace yana kawo kwanciyar hankali. Ta zaman lafiya ake samun yin hulda da 'yanuwa da abokan arziki.

Alhaji Hassan ya kira masu tada zaune tsaye su gane cewa a duniyar nan babu abun da ya fi zaman lafiya dadi da kwanciyar hankali. Ya ja kunnuwan 'yan Najeriya su nemi zaman lafiya da juna ko ta halin kaka musamman a wannan watan mai albarka.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:51 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG