Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Buhari Ya Rarraba Kawunan ‘Yan Najeriya Ba: Adesina


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Fadar shugaban kasar Najeriya ta maida martani kan kushewa gwamnatin da ake yi cewa, ta kara rarraba kawunan ‘yan Najeriya.

Mai ba shugaba Muhammadu Buhari shawarwari kan harkokin sadarwa da hulda da jama’a Femi Adesina, ya musanta wannan zargin a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Channels jiya Laraba.

Da yake maida martani kan kalaman tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, da kuma na fitaccen marubucin Najeriya wanda ya sami lambar yabo ta Nobel Farfesa Wole Soyinka, wadanda suka bayyana takaicin rarrabuwar kawuna da tsatsaguwa da ake ci gaba da samu a kasar da suka ce, ta kara ta’azzara karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari, Adeshina yace, idan za a yi la’akari da kalaman tsohon shugaban kasar da kuma na Farfesa Shoyinka a lukutan baya, za a fahimci cewa, an dade da samun rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan Najeriya . Femi Adeshina ya bayyana cewa, babu wani lokaci a tarihin Najeriya da kasar ta ke hade tun daga shekara ta dubu dari tara da goma sha hudu.

shugaba-muhammadu-buhari-ya-gaza-obasanjo

buhari-ya-mayar-wa-da-obasanjo-martani

Yana mai cewa, “A lokacin da Shugaba Buhari ya hau mulki a shekata ta 2015, ana matukar fuskantar rarrabuwar kawuna a Najeriya kama daga banbancin addini, da kabilanci, da banbancin harsuna da rarrabuwar kawuna ta kowacce fuska. Abinda Shugaban kasar ya ke fama da su ke nan. Kuma ka ga, a maimakon wadansu mutane su bari a sami hadin kai a wannan kasar, suna kokarin kara fadin gibin da ke akwai. Suna sa siyasa a cikin komi.”

Farfesa Wole Soyinka, ya fitar da sanarwa ranar Talata, kwana biyar bayan kasidar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gabatar a wani taron tuntuba da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, inda ya zargi shugaba Buhari da kara rarraba kawunan al’ummar kasar.

Farfesa Wole Soyinka
Farfesa Wole Soyinka

A cikin sanarwar da marubucin ya rattabawa hannu, ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasar ba ya burge shi, sai dai yace, ya yarda da duk wanda zai fadi gaskiya dangane da halin da Najeriya ke ciki.

Ya ce,“Ni ban damu da Olusegun Obasanjo ba, janar na soja, wanda ya yi shugabancin Najeriya har sau biyu, kuma daya daga cikin shugabannin da suka kawo koma bayan kasar da ake kira Najeriya. Ba ni da dalilin canza matsayi ta a kan irin abinda ya yi, duk da haka, ina da hakkin jawo hankali kan duk wani abinda aka fada da ya zama gaskiyar halin da kasar nan ke ciki ko daga wanne tushe ta fito, domin ceto kasar daga rugujewa” Farfesa Soyinka ya tunatar da ‘yan Najeriya su saurari gargadin da tsohon shugaban kasar ya yi a shekarar da ta gabata domin ceto kasar.

A maida martaninsa kan takardar da Farfesa Soyinka ya rubuta, Adesina ya ce dama marubucin bai taba boye cewa ba ya ra’ayin Buhari ba tun lokacin Buhari na shugaban mulkin soja.

Adesina ya ce a kasa mai mutane sama da miliyan dari biyu, ba shi yiwuwa ra’ayi ya zo daya.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG