Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Mayar wa Da Obasanjo Martani


Buhari,hagu da Obasanjo, dama
Buhari,hagu da Obasanjo, dama

A Najeriya, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obansajo wanda ke sukar lamirin gwamnati mai ci yayin da ita kuma take zargin sa da yunkurin rarraba kawunan 'yan Najeriya a martanin da ta mayar masa.

Fadar gwamnatin shugaban Najeriya ta mayar da martani ga tsohon shugaba kasar Olusegun Obasanjo dangane da sukar lamirin gwamnatin da ya yi tana mai cewa kalaman tsohon shugaban “yunkuri ne na haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umar kasar.”

Wata sanarwa dauke da sa hannun malam Garba Shehu da ke magana da yawun shugaba Buhari da fadar ta fitar a ranar Lahadi ta yi gugar zana kan yadda Obasanjo ya zubar da kimarsa.

“Banbancin ya bayyana karara. Daga mukamin babban kwamandan dakarun kasa, Janar Obasanjo ya yada girmansa ya koma shugaban masu raba kawuna.”

A ‘yan kwanakin da suka gabata ne, Obasanjo ya yi ikrarin cewa ba a taba samun rarrabuwar kawuna da koma baya a Najeriya ba, kamar yadda ake fuskanta karkashin mulkin shugaba Buhari.

Tsohon shugaban ya kuma bayyana takaicin ganin yadda talauci ya yi kamari a kasar da yanzu ake bayyanawa a matsayin kasar da ta fi kowacce kasa talauci a duniya.

Kalaman na Obasanjo na zuwa ne yayin yake gabatar da kasida a wani taro da aka gudanar a birnin Tarayya na Abuja mai taken “Ceto Najeriya daga kifewa.”

Taron tuntubar ya sami halartar manyan kungiyoyi daban- daban na yankunan kasar da suka hada da, kungiyoyin hadin kan Yarbawa da aka fi sani da Afenifere, da kungiyar dattawan arewacin Najeriya, Northern Elders Forum.

Sauran kungiyoyin sun hada da ta shugabannin kalibar Igbo, Ohanaeze Ndi Igbo, da kungiyar hadin kan jihohin arewa ta tsakiya, Middle Belt Forum, da kuma kungiyar hadin kan al’ummar yankin Naija Delta, Pan Niger Delta Forum.

Sai dai sanarwar fadar gwamnatin ta Najeriya, ta tunatar da Obansanjo kan yadda ya yi yunkurin yin tazarce abin da “shugaba Buhari yake ba shugabannin yankin yammacin nahiyar Afirka da su guji yi domin ya sabawa tsarin doka.”

“Ko da yake, (Obasanjo) ya taba gwadawa bai yi nasara ba, amma yadda ake samun karin shugabannin suna nuna bukatar su yi tazarce ko kuma suka yi tazarce, na zama abin damuwa a tsakanin masu muradin kare tsarin dimokradiyya a yankin, idan aka yi la’akkari da yadda hakan ke haifar da rudani a kasashe da yankin baki daya.” sanarwar ta kara da cewa.

Kakakin shugaba Buharin ya kara da cewa, “kamar yadda wasu masu sharhi kan al’amuran yau da kullum ke ba da shawara, kamata ya yi Cif Obasanjo ya yi koyi da wa’azin da yake yi a matsayinsa na dattijon kasa, ya mayar da hankalinsa kan samar da maslaha kan matsalolin da ke akwai, ba wai ya rika rura wutar kabilanci da banbancin addini ba.”

A cewar Garba Shehu, babu shakka, da yawa daga cikin magoya bayansa na gida da waje, sun ji mamaki da ya yabi wasu daga cikin kungiyoyin da suka sha alwashin kin karbar goron gayyatar da za a aika masu zuwa zauren majalisar dokokin kasa domin su ba da gudunmowarsu wajen yin garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Cif Obasanjo ke sukar lamirin gwamnatin ta Buhari ba domin ko a baya ya sha rubuta mai budaddiyar wasika yana nuna gazawarsa.

Sannan ba gwamnatin Buhari kadai Obasanjo ya taba suka ba domin ko a baya ya sha caccakar gwammatin tsohon shugaba Good Luck Jonathan.

A shekarar 2013, Obasanjo ya taba rubuta wasika mai shafuka 18 ga tsohon shugaban kasa Jonathan inda ya zayyana dalilai 10 da ya sa ya rubuta budaddiyar wasikar yana mai kira a gare shi da ya yi gyara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG