Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Gaza: Obasanjo


Buhari na Obasanjo
Buhari na Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza hada kan kasa da kuma samar da shugabancin kwarai.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana haka ne yayin gabatar da kasida a wani taro da aka gudanar a birnin Tarayya Abuja da taken “Ceto Najeriya daga kifewa” taron tuntubar da ya sami halartar manyan kungiyoyi dabam dabam na yankunan kasar da suka hada da, kungiyoyin hadin kan Yarbawa da aka fi sani da Afenifere, da kungiyar dattawan arewacin Najeriya , Northern Elders Forum, da kungiyar shugabannin kalibar Igbo, Ohanaeze Ndi Igbo, da kungiyar hadin kan jihohin arewa ta tsakiya, Middle Belt Forum, da kuma kungiyar hadin kan al’ummar yankin Naija Delta, Pan Niger Delta Forum.

Obasanjo ya ce ba a taba samun rarrabuwar kawuna da koma baya a Najeriya ba, kamar yadda ake fuskanta yanzu karkashin mulkin shugaba Buhari, ya kuma bayyana takaicin ganin yadda talauci ya yi Kamari a kasar da yanzu ake bayyanawa a matsayin kasar da tafi kowacce kasa talauci a Duniya.

Yace “Naji ji dadi da dukan ku, ku ke bakin ciki da kuma jin kunya kamar yadda galibin mu, ‘yan Najeriya mu ke ji game da halin da muka tsinci kanmu. Najeriya tana kan hanyar zama kasar da ta gaza, da kuma ke fuskantar mummunan rarrabuwar kawuna.A fannin tattalin arziki, kasarmu ta zama abinda tausayi, inda talauci ya fi Kamari a duniya. Mun kuma kasance kasar da ake fama da rashin tsaro. Wadannan kuma alamu ne na rashin shugabancin kwarai da rashin kyakkyawan amfani da albarkatu iri dabam dabam da muke da su wajen gina kasarmu. Tsofaffin dabi’un da suka janyo koma baya da aka fara mantawa da su, yanzu sun sake kunno kai suna assasa gaba da kiyayya a ko’ina”

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Bisa ga cewar tsohon shugaban kasar, duk wani mai hankali da kishin kasa ya san cewa, al’amura basu tafiya daidai a Najeriya. Ya kuma caccaki ‘yan siyasa a kasar da suka fara tunanin zaben shugaban kasa na shekara ta 2030 a maimakon kokarin tunkara matsalolin da suka addabi kasar da neman hanyar magance su. Yace tilas ne a nemi hanyar kaiwa shekara ta 2030 ta wajen neman hanyoyin kawo karshen mace mace, da barna, da lalata kaddarori, da ficewa daga basusuka, da cututuka, da yaudara, da rashin gamsuwa, da rashin yarda dake tsakanin al’umma. A kuma hada kai a zama kasa mai buri daya, kafin a yi tunanin shekara ta 2030.

Ya kuma yi kira ga wadanda suke kara yayata akidar da ke cusa ra’ayin da zai kai ga rarraba kawuna da kuma gaba a kasar, da su sani cewa, ko Najeriya ta ruguje, bangarorin zasu ci gaba da zama makwabtan juna, sabili da haka tilas su koyi zama lafiya da juna idan ba baka ba zasu zama makwabtan da zasu rika yakar juna iya rayuwarsu. Yace duk wadanda suka toshe kafar adalci suna gayyatar tashin hankali ne.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasar ya sha sukar gwamnatin Buhari musamman kafin zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara lokacin da Buhari ya sake tsayawa takarar neman wa’adin mulki na biyu.

A watan Yuli shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, tsohon shugaban kasar ya rubuta budaddiyar wasika ga shugaba Buhari kan matsalar tsaro inda ya bayyana cewa, “batun da na ke magana a kai a nan matsala ce babba. Batu ne da ya shafi rayuwa ko mutuwa a gare mu duka da kuma kaunatacciyar kasar mu, Najeriya. Ba za a ci gaba da watsi da wannan batun, ko nuna halin ko in kula, ko shafa ma shi mai ba. Batun yana barazana ga ci gaba da kasancewar mu ‘yan Najeriya, da kuma shafar tushen al’ummarmu. Na damu matuka da kuma fargaban ganin yadda muke nufar wani matsayin da zai yi wuya mu kaucewa fadawa cikin hadari…, a matsayin dan Najeriya wanda ya ke yawo da tabon yakin basasan Najeriya a jikina, da kuma wanda dansa ya ke yawo da tabon yaki da kungiyar Boko Haram a jikin sa, ina fata zaku fahimci abinda ya sa na damu.”

Ya kara da cewa, “idan hankalin mutane ya tashi, suna kuma jin basu da kwarin guiwa cewa gwamnati zata iya tsare rayuka da kaddarorin su, zasu dauki kowanne irin matakin kashin kansu da kuma na hadin guiwa wajen kare kansu.”

matsalar-tsaro-na-barazana-ga-hadin-kan-najeriya

obasanjo-ya-kwatanta-gwamnatin-buhari-da-ta-abacha

A shekara ta dubu biyu da goma sha uku, tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya taba rubuta wasika mai shafuka 18 ga tsohon shugaban kasa Gooluck Jonathan inda ya zayyana dalilai 10 da ya sa ya rubuta budaddiyar wasikar ga shugaba Jonathan. A cikin wasikar Obasanjo ya ce, “tilas ne Jonathan ya nisanta kansa da abinda zai kawo tsatsaguwa da raba kan kasa tsakanin Kudu da arewa, da kuma Musulmi da Kirista.” Ya ce “bai kamata a yi wani abu da zai jefa kasar cikin komadar tattalin arziki, ko kuma maida hannun agogon baya ba.”

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A cikin budaddiyar wasikar da Obasanjo ya rubutawa Goodluck Jonathan, ya ce “wadanda suke baka shawara ka kuntatawa wadanda su ke adawa da kai, sune manyan abokan gabanka. Siyasar Damokaradiya tana rungumar ‘yan adawa da kuma sauraron magoya baya da kuma ‘yan hamayya. Idan aka shiga matsala, wadanda suka ba ka gurguwar sha’awara ba za su tsaya su taimake gumi ba. Tilas ne a koyi darasi daga Misira.”

Yayinda wadansu suke yaba gargadin da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ke yi kan halin da kasa ta ke ciki, wadansu da dama suna gani ba komi ba ne illa neman wuce makadi da rawa da kuma laifi tudu- ta kata naka ka hangi na wani, da cewa, shi ma mulkinsa yana cike da kura-kurai.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG