Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Yi Hatsari Ba, Muna Nan Cikin Koshin Lafiya – Sarkin Waka


Nazir Sarkin waka (Instagram/Nazir Sarkin Waka)

A ranar Litinin wasu shafukan sada zumunta suka wallafa bayanan boge da ke nuna cewa mawakin ya gamu da hatsarin mota kuma har ya rasa ransa.

Fitaccen mawakin Hausa Nazir Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya mayar da martani ga masu yada jita-jitar cewa ya mutu a hatsarin mota.

A ranar Litinin wasu shafukan sada zumunta suka wallafa bayanan boge da ke nuna cewa mawakin ya gamu da hatsarin mota kuma har ya rasa ransa.

Amma a wani martani da ya mayar a shafinsa na Instagram, fitacce mawakin ya kalubalanci masu yada jita-jitar.

“To saurin me kuke yi? Allah ya shirye ku, mu kuma ya kyautata karshenmu. Amin.” Sarkin waka ya wallafa a shafinsa na Instagram hade da wani hoto da ke nuna wasu motoci farare sun yi hatsari.

Bayan wasu sa’o’i ne kuma mawakin ya sake wallafi wani sako yana mai sake musanta rade-radin cewa ya yi hatsarin.

“Alhamdulillahi, ba mu yi hadari ba, kuma muna nan cikin koshin lafiya.”

Wannan dai ba shi ne karon farko da wasu shafukan sada zumunta suke wallafa bayanan boge da ke nuna cewa wani fitaccen jarumin Kannywood ya mutu ba.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG