Accessibility links

Babban Bankin Najeriya Ya Kara Wa'adin Sabunta Asusun Masu Ajiya a Bankuna


Masu hada-hadar kudi ta bayan fagge

Bankunan Najeriya sun cika da dogayen layi soboda kokarin da jama'a ke yi su samu su sabunta asusunsu kafin lokacin da babban bankin kasar ya kayyade.

Dubban mutane da suka mamaye bankuna yau sun sanya harkokin kasuwanci da na kudi sun tsaya cik.

Ta bakin wasu mutane sun cika bankuna da yawa lamarin da ya sha kan ma'aikatan. Idan ba su bankuna sun kara ma'aikata ba to da wuya su kammala aikin cikin lokacin da aka bayar.

To saidai sanarwar da shi babban bankin ko CBN ya fitar na cewa ba za'a hana masu ajiya su cire kudadensu kamar yadda ake ta raderadi koda kuwa basu yi rajistan ba.

Amma rashin rajistan zai shafi hada-hadar kudadensu wajen aikewa da kudi ta waya ko kuma ta naurar kwamfuta. Haka ma masu makudan kudaden ajiya da suka haura nera miliyan dari rashin rajistan zai shafesu.

Yanzu dai babban bankin ya kara wa'adin rajistan da wata hudu zuwa 31 ga watan Oktoban wannan shekarar. Ana fata cikin karin lokacin kowa zai yi rajista ya kuma samu lamba mai suna BVN.

Ga rahoton Babangida Jibrin.

XS
SM
MD
LG