Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sakataren Kungiyar CAN Ta Najeriya Ya Rasu


Rev Dakta Musa Asake

Babban sakataren kungiyar hadin kan Krista ta Najeriya CAN, Rev Dakta Musa Asake ya rasu ranar Juma’a.

A wata sanarwa da ke da sa hannun mataimaki na musamman a bangaren yada labarai ta kungiyar CAN, Pastor Adebayo Oladeji, a madadin shugaban kungiyar tace marigayin ya rasu ne bayan wata garejiyar rashin lafiya.

An haifi Rev Musa Asake ne ranar 15 ga watan Satumba 1952, a unguwar Rimin Bajun Kafanchan dake karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

Aikin marigayin na karshe a matsayin sakataren CAN shine taron ‘yan jarida da ya gudanar a ‘yan kwanaki da suka gabata, inda ya koka kan irin kashe-kashe da zubda jini da ke faruwa a Najeriya, inda CAN ta yi kiran ayi zanga-zangar lumana don zaburar da gwamnati ta yi aikinta.

Marigayin yayi aiki a matsayin sakataren darikar ECWA dake da hedikwata a birnin Jos. Kafin wannan aikin yayi aiki limanci a Majami’u daban-daban a fadin Najeriya.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG