Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Cibiyar Wutar Lantarki Mai Amfani Da Hasken Rana Ta Fara Aiki A Nijar  


Cibiyar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mafi girma a Nijar.
Cibiyar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mafi girma a Nijar.

Ana samun makamashin hasken rana sosai a Nijar, yankin da ke kudu da Sahar hamada a yammacin Afrika. Akwai farantan tatsar hasken rana fiye da 55,000 da aka sanya a cibiyar. 

Cibiyar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mafi girma a Nijar ta fara aiki, a cewar ministan makamashin kasar ranar Lahadi, lamarin da zai taimaka wajen saukaka karancin wutar lantarki da ake fuskanta a kasar tun bayan da Najeriya ta dakatar da ba Nijar din wutar lantarki bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023.
A cewar kamfanin dillancin labaran AFP na Faransa, ministan makamashin Nijar Mahaman Moustapha Barke, ya fada ta talabijin na kasar cewa kamfanin samar da wutar lantarkin kasar da ake kira Nigelec, tuni ya lura an samu "ingantuwar wutar lantarki" a Yamai babban birnin kasar, da Dosso, da kuma Tillaberi.

Ana samun makamashin hasken rana sosai a yankin mai hamada dake yammacin Afrika. Akwai farantan tatsar hasken rana fiye da 55,000 da aka sanya a cibiyar, kuma suna iya samar da megawatt 30 na wutar lantarki.
Galibin sassan Nijar sun fuskanci daukewar wutar lantarki a kai a kai bayan da Najeriya ta daina kai musu lantarki, a zaman wani bangare na takunkumin da kasashen yankin suka sanya wa jagororin juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.
kamfanin Nigelec na sayen kashi 70 cikin 100 na wutar lantarki daga Najeriya kafin juyin mulkin, a cewar wani rahoto na shekarar 2022 da kamfanin wutar lantarkin Nijar guda daya tak ya fidda.

Nijar ta kuma fara aikin gina madatsar ruwa ta farko a kogin Neja domin rage dogaro da makamashin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG