Accessibility links

Babbar Jam'iyyar Hamayya ta APC Tana Cigaba da Rijistar Magoya Bayanta

  • Aliyu Imam

Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubnakar Yana daga cikin wandanda suka yi rijista.

Alhamis din nan ne aka shiga wuni na biyu na rijistar 'ya'yan babbar jam'iyyar hamayya ta APC a duk fadin Najeriya. Saboda haka ne majalisar dattijan Najeriya ta dage zamanta don baiwa magoya bayan jam'iyyar damar komawa mazabunsu domin shirin rijistar.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yana daga cikin wadanda aka yiwa rijista, har yayi amfani da damar wajen maida martani kan zargin da tsohuwar jam'iyyarsa PDP take yi cewa ai zai koma jam'iyyar.

Alhaji Atiku ya gayawa wakilin Sashen Hausa Ibrahi Abdulazizi cewa kada ma ya saurari maganganun PDP domin kamar yadda yace "ta yi nisa bata jin kira".

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG