Accessibility links

Canza Shekar da Wasu Sanatocin PDP Suka Yi Ya Jawo Takaddama a Majalisar Dattawa


Ginin Majalisun Dokokin Najaeriya

Makon jiya ne wasu sanatocin PDP suka yi ikirarin barin jam'iyyar zuwa ta APC to amma lamarin ya jawo takaddama amajalisar dattawa

Takaddamar da ta kunno kai sabili da canza shekar da wasu sanatocin PDP suka yi ya sa majalisar ta kwashi sa'o'i biyu da rabi tana muhawara.

Sanato Ibrahim Kabiru Gaya daga jihar Kano ya yi karin haske a kan lamarin. Ya ce abun da ya damesu shi ne batun canza sheka da wasu sanatocin PDP suka yi zuwa jam'iyyarsu. A doka an sha yin hakan kuma ba'a taba samun rikici ba sai a wannan karon. Amma yanzu an samu damuwa daga bangaren PDP domin basa son sanatocin su bar jam'iyyar bayan su sanatocin sun tabbatar sun bar jam'iyyar sun kuma sa hannu a takarda sun ba kakakin majalisar.

Tambaya a nan ita ce menene dokar majalisa a kan irin wannan lamarin? Solomon Ewuga dan majalisar dattawan ya ce a dokokinsu sai an tabbatar da iyakan mutanen domin daga farko an ce su 17 sai gashi ana batun mutane 11. Don haka dole kowa ya sa hannu a tabbatar. Dangane da kundun tsarin majalisar ko na kasa Yushau Waziri Mamman lauya mai zaman kansa kuma kwararre kan kundun tsari ya yi karin haske. Ya ce idan an dubi kundun tsarin mulkin kasa ya ba kowa izinin ya hada kai da kowa ba tare da tsangwama ba kan addini ko bangaranci ko kabilanci. Amma idan aka dubi kundun tsarin mulki na jam'iyyun wato PDP da APC sun ce idan zaka bar jam'iyya ba zaka yi kai tsaye ba sai dai idan akwai baraka a cikin jam'iyyar . Idan akwai baraka kana da daman ka koma wata jam'iyya. Wasu dake barin PDP sun ce akwai baraka amma kotu ta yanke hukunci kwanan nan cewa babu baraka a PDP. Wasu sun daukaka kara a kai kuma watakila maganar zata kai har kotun koli.

XS
SM
MD
LG