Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kotun Kano Ta Dakatar Da Majalisar Dokokin Kanon Binciken Ganduje


Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano
Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

Babbar Kotun Kano ta umarci majalisar dokoki ta jihar ta dakata da binciken zargin rashawar Dala miliyan biyar akan gwamna Abdullahi Umar Ganduje, har sai ta saurari karar da wasu lauyoyi suka shigar gaban ta. sai dai majalisar tace ba ta kai ga samun wannan umarni ba.

Wata kungiyar lauyoyi mai rajin wanzar da tsarin mulkin demokaradiyya a Najeriya wato Lawyers for Sustainable Democracy in Nigeria itace ta shigar da kara gaban babbar kotun Kano tana kalubalantar majalisar game da wannan batu.

Baya ga majalisar dokokin, kungiyar lauyoyin ta shigar da kara ga Atoni Janar kuma kwamishinan shari’a na Kano kana da shugaban kwamitin da majalisar dokokin ta kafa na bincikar wannan batu na rashawa a kan gwamnan Kano.

Barrister Mohammed Ma’aruf shine lauyan dake bada kariya ga gwamna Ganduje a gaban kwamitin bincike na majalisar.

Ko me wadannan lauyoyin rajin demokaradiyya ke muradin cimmawa har suka tafi kotu? Barrister Zubair ya bada karin haske akai

Sai dai duk da haka majalisar dokokin ta ce bata da masaniyar wannan kara a hukumance. Hon Baffa Babba DanAgundi shine shugaban kwamitin binciken da majalisar keyi.

A baya dai yau ne talata majalisar dokokin ta Kano ta tsara fara aikin tantance faifen bidiyon zargin rashawar dala miliyan 5 akan gwamna Ganduje daga hannun ‘yan kwangila.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari a kan wannan batu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG