Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Haure 800 Daga Afirka Sun Dunguma Zuwa Iyakar Morocco da Ceuta


Jami'an tsaro na gadin iyakar Spaniya
Jami'an tsaro na gadin iyakar Spaniya

Akalla bakin haure 800 daga yankin Afrika na kasashen dake kudu da Sahara, sun dunguma zuwa kan iyakar Morocco da Ceuta, wani dan karamin birni mai cin-gashin kansa dake kasar Spaniya, a cewar hukumomin Moroccon da na Spaniyan.

Tattaki da suka yi zuwa wannan yanki, ya haifar da arangama tsakanin su da jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga jikkata ‘yan sandan Spaniya biyar da kuma na Morocco 50.

Bakin hauren sun yi yunkuri ne su kawar da wani shingen da aka kafa a kan iyakar kasashen biyu domin shiga nahiyar turai.

Hukumomi sun ce an bar wasu bakin haure biyu sun shiga yankin na Ceuta domin karbar magani bayan da suka ji rauni a arangamar.

Amma kuma an tisa keyar sauran daruruwan bakin hauren zuwa inda suka fito, lamarin da ke janyo suka daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama.

Hukumar dake kula da bakin haure ta duniya ta ce a bara akalla bakin haure 5,000 ne suka mutu a tekun Meditareniya, wanda haka ya sa shekerar ta 2016 ta zamanto mafi muni ga bakin haure.

XS
SM
MD
LG