Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bala'in Amai Da Gudawa A Sansanonin 'Yan Gudun Hijira A Jihar Flato


Wata mata 'yar Nigeria ce ke kallon gidajen da aka kokkona a lokacin rikicin zaben Nigeria a kauyen Kachia, kudancin jihar Kaduna.
Wata mata 'yar Nigeria ce ke kallon gidajen da aka kokkona a lokacin rikicin zaben Nigeria a kauyen Kachia, kudancin jihar Kaduna.

A dai dai lokacinda jihar Flato ta kai doki ga 'yan gudun hijira daga jihar Nasarawa da suke jihar, cutar amai da gudawa ta bulla a sansanoninsu.

Gwamnatin jihar Flato ta kashe kimanin Naira milyan 20 domin samarda kayan agaji ga samada 'yan gudun hijira su dubu bakwai da suke sansanoni daban daban cikin jihar.

A dai dai lokacinda gwamnatin take kai musu wannan doki, sai ga shi an sami labarin cutar amai da gudawa ta bulla a wasu sansanonin da 'yan gudun neman mafakan suke a Namu, Kwande, da bakin cibiya, cikin karamar hukumar Qwanpam.

Da take magana da wakiliyar Sashen Hausa Jamila Lawal, tace suka cikin damuwa kwarai, da suka hada d a rashin kudi, ka mata masu juna biyu kusan sittin wadanda suka haifu a sansanonin ga kuma karancin kiwon lafiya cikin yanayi d a suke ciki. Tace ko sisi mutum ba ya iya tayarwa balle suyi tunanin baiwa yara ko da kudin kashewa. Da take amsa tambayar batun makaranta sai tace ai basu da kwanciyar rai balle kuma a yi zancen unifom da yara domin zuwa makaranta.

Da yake magana kan gudumawarda gwamnatin jihar Flato ta samar, sakataren hukumar agajin gaggawa na jihar Flato Alhassan Barde, yace tallafawa 'yan gudun hijirar ya zama wajibi domin baya ga kasancewarsu mutane daga jiha makwabciyar jihar wadanda suka fada cikin mawuyacin hali, ita jihar Flaton ba a juma ba da ta sami kanta cikin irin wannan yanayi.

Mr. Barde yayi alkawarin gwamnatin zata tabbatar da cewa kayayyakin agajin sun kai ga wadanda aka saya dominsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG