Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Halaka 'Yan sanda a Masar


Wasu 'yan sandan Masar suna gadin wani wuri da aka kai harin bam, ranar 28 ga watan Disamba, 2018.

‘Yan sandan biyu na bin mutumin ne wanda ke dauke da wani abu mai fashewa, wanda ya tarwatse a kusa da Masallacin Al Azhar.

Wasu ‘yan sandan kasar Masar biyu sun rasa rayukansu bayan da wani abin fashewa ya tarwatse a hannun wani mahari da suke bi a tsakiyar birnin Alkahira.

Mutumin ya mutu sannan wasu mutum uku sun jikkata.

Jami’an tsaro sun ce ana zargin maharin da laifin yunkurin kai harin bam akan ‘yan sanda a birnin na Alkahira a makon da ya gabata.

‘Yan sandan biyu na bin mutumin ne wanda ke dauke da wani abu mai fashewa, wanda ya tarwatse a kusa da Masallacin Al Azhar.

A ranar Juma’a aka zargi mutumin da yunkurin dasa bam a birnin Alkahira, wanda jami’an tsaro suka gano suka kuma kwance shi.

Facebook Forum

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG