Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ki-moon Ya Gana Da Shugaba Muhammadou Issoufou a Yamai


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Babban sakataren MDD, Ban Ki-moon ya jaddada muhimmancin yankin Sahel, yayin da shugabannin cibiyoyin duniya suka bayyana ba shirin kashe Euro miliyan 181 a Nijar kawai

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Ban Ki-moon, da tawagarsa ta manyan jami'an cibiyoyin gwamnati da na kudi na duniya sun gana da shugaba Mahamdou Issoufou na Jamhuriyar Nijar, yau a birnin Yamai, a ci gaba da rangadin kasashen yankin Sahel guda biyar da tawagar keyi.

A bayan ganawar da suka yi a fadar shugaban kasa, Mr. Ban da shugaba Issoufou tare da sauran jami'ai sun zarce zuwa majalisar dokoki ta kasa a inda suka gudanar da taron 'yan jarida na hadin guiwa.

Babban sakataren MDD, yace yankin Sahel ya shiga idanun duniya a bayan abubuwan da suka wakana a kasar Mali, kuma a yanzu duniya ta san cewa yankin yana fama da matsaloli na tsaro, makamashi, noma, kiwo da sauransu. Don haka ne majalisar, tare da hadin kan babban bankin duniya, da bankin raya kasashen Afirka, da Majalisar tarayyar Turai suka hadu domin kirkiro da shirin tallafawa yankin na tsawon shekaru 7.

A Jamhuriyar Nijar kawai ma, cibiyoyin zasu bayar da tallafin Euro miliyan 181 domin gudanar da wadannan ayyukan, wadanda kuma sun hada har da samar da wadataccen abinci da ruwan sha.

Shugaba Mahamadou Issoufou yace wannan tsari na MDD ya dace da irin shirye-shiryen shugabannin yankin na Sahel, kuma zai tallafa ma yunkurin shugabanni da al'ummar yankin na wanzar da tsaro da kawar da talauci.

Daga bisani, babban sakataren na MDd, Ban Ki-moon, ya gabatar da jawabi mai ratsa jiki a gaban majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar.

Tuni tawagar ta wuce zuwa kasar Burkina Faso.

Ga Abdoulaye Mamane Ahmadou da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG