Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon Ya Roki 'Yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Su Kai Zuciya Nesa


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon yana kira ga al’umar kasar Afirka ta tsakiya su kawo karshen tarzomar da yace ta kai kasar dab da wargajewa.

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon yana kira ga al’umar kasar Afirka ta tsakiya su kawo karshen tarzomar da yace ta kai kasar dab da wargajewa.

A cikin wani jawabi ta vidiyo da ya yiwa al’umar kasar jiya jumma, Mr. Ban yace “hankalinsa ya yashi matuka” kan irin al’amura da suke wakana a kasar, daga nan ya “kira yi kowa da kowa da ya bi hanyar da zata kai ga wanzarda zaman lafiya.”

Babban magatakardan yayi magana ne jim kadan bayanda ofishin kwamishinan kare hakkin Bil’Adama na MDD ya bada rahoton cewa an sami karuwar zaman dar dar tsakanin al’umar musulmi d akirista a kasar.

A cikin wani bayani da kakakin ofishin kiyaye hakkin BIl’Adama ta majalisar Ravina Shamdasani tayi, tace an kashe musulmi 27 akauyen Bohong dake yammacin kasar. Tace bisa dukkan alamu ‘yan kungiyar nan da ake kira ta masu adawa da Balaka, wadanda galibinsu kiristoci ne, su suka kashe musulman ranar Alhamis. Haka kuma kakakin ta bada labarin cewa akwai rahotannin da suke nuna cewa an dauki fansa kan wannan hari tsakanin kiristoci da musulmi da suke da zama a Banqui babban birnin kasar cikin ‘yan kwanaki da suka wuce.

A cikin jawabin nasa ta vidiyo Mr. Ban yace mutan kasar jamhuriyar Afirka kada su kyale ‘masu haddasa husuma’ su dasa gaba da banbance banbance da ada babu su tsakanin jama’a.
XS
SM
MD
LG