Accessibility links

Akwai banabancin ra'ayi game da ziyarar Shugaba Obama zuwa nahiyar Afirika tsakanin 'yan Najeriya dangane da yadda ya yi watsi da kasar.

Yayin da Shugaban Amurka Barack Obama ke cigaba da ziyararsa a nahiyar Afirika 'yan Najeriya na bayyana ra'ayoyi daban-daban dangane da yadda ya yi watsi da kasar.

Ra'ayoyin 'yan Najeriya sun rabu gida biyu.Yayin da wasu ke ganin yakamata Obama ya zo Najeriya shi ko wani tsohon kwamishana a Jihar Neja Basarake Umaru Lagada gani yake a yanayin rashin tsaro a Najeriya bai kamata ya zo ba. A cewarsa zuwan Paparoma ma ya fi zuwan Obama domin ko ba komi kasar zata samu addu'a. Ya ce ko yazo ba kudi ba ne zai kawo kasar. Zai zo ne ya kalli menene bukatun Amurka a Najeriya ya yi kokarin karesu. Shi ko Aliyu Mohammed cewa ya yi yakamata a ce ya zo domin zai zama karin muhibba ga gwamnatin mai ci yanzu da ma kasar. Rashin zuwansa zai iya zama nakaso ga kasar. Kasancewar Amurka kasa ce mai jagorancin duniya ko ba'a ci ribar zuwanshi yanzu ba za'a ci nan gaba. Dangantaka tsakanin kasashen biyu zata kara kwari.

Amma wasu 'yan kasuwa fata suke Allah ya sa ziyarar ta Shugaba Obama ta sa shugabannin Afirika su rage masu kudin harajin da suke biya kan kayan da suke shigowa da su daga kasashen waje. Alhaji Mustafa Austo dan kasuwa mazaunin Minna cewa ya yi idan mutum ya je kasar Indiya ko Du Bhai ko Sin ya sawo kaya to duk wanda ya sama hannu so yake ka bashi kudi. A karshenta dan kasuwa sai ya fadi maimakon ya ci riba. Yan kasuwa kama daga wadanda suke shigo da kaya iri-iri zuwa ga masu shigo da motoci sun yi korafin haraji mai yawa da gwamnati take dora masu.

Mustafa Nasiru Batsari na da karin bayani.

XS
SM
MD
LG