Accessibility links

Shugaba Barack Obama Na Amurka Na Ziyara A Afirka

  • Ibrahim Garba

Shugaba Barack Obama da matarsa Mechelle a kan hanyarsu ta ziyara a kasashen Afirka

Shugaba Barack Obama na Amurka ya sauka kasar Senegal a zangon farko na ziyararsa a kasashen Afirka.

Shugaba Barack Obama na Amurka yana kasar Senegal, zangonsa na farko a rangadin habaka huldar cinikayya, zuba jari da kuma samar da wadataccen abinci a nahiyar Afirka.

Abubuwan da aka tsara shugaban zai gudanar yau alhamis sun hada da liyafar cin abincin xdare da shugaba Macky Sall na Senegal tare da tattaunawa kan batun mulki bisa doka da shugabannin bangaren shari’a na yankin Afirka ta yamma.
Har ila yau, shugaba Obama da maidakinsa Michelle zasu ziyarci tsibirin Goree, wanda Hukumar Ilmi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a zaman Wurin Tarihi na Duniya, wanda kuma daga karni na 15 har zuwa karni na 19, ya kasance cibiyar jigilar bayi daga Afirka zuwa Turai ko nahiyoyin Amurka mafi girma a duk tsawon gabar nahiyar.

Fadar White House ta bayyana Senegal a zaman kasar dake kunno kai a tafarkin dimokuradiyya, kuma kawar Amurka wajen gina cibiyoyin dimokuradiyya a Afirka.
A lokacin da yake magana kan wannan rangadi na shugaban Amurka, babban jami’in huldar cinikayya tsakanin Amurka da kasashen duniya, Michael Froman, yace a yayin da annobar cutar kanjamau ta ke ja da baya, kuma ake samun raguwar cin hanci da rashawa, taurarin Afirka sun fara haskakawa a fagen yunkurin rage talauci.
XS
SM
MD
LG